Wani matashi ya tambayi abokinshi, ina kake aiki? Sai yace: wuri kaza. Abokin yace : Nawa ake baka a wata? Yace:- 5000. Sai abokin yace : 5000 kadai? Tayaya zaka rayu da dubu biyar? Tun daga wannan ranar abokin ya raina aikinshi, ya nemi a qara mashi albashi, mai gidan yaqi qara mashi, shi kuma ya watsar da aikin. A da yana aiki, yana samun 5000 a wata, amma yanzu baya aikin komai. ✍️Wata ta tambayi qawarta wace kyauta mijinki ya baki a ranar birthday dinki? Sai tace bai bani komai ba. Shine qawar tace : Da gaske kike? Anya kina da daraja a wurinshi kuwa? Tunda ta jefa mata wannan bomb din a gida ta fita, da mijin matar nan ya dawo ya tadda ta cikin fushi, suka hau rigima da jayayya daga qarshe ya sake ta. Daga ina matsalar ta fara? Daga wannan kalmar da qawarta ta gaya mata. ✍️Ance akwai wani mahaifi da yake rayuwa cikin kwanciyar hankali da iyalanshi, sai abokinshi yace mashi, ya akai danka bai ziyartarka sosai? Anya rashin lokaci ne ko ko dai baya sonka? Tun daga wannan ...