Skip to main content

RUSHEWAR GIDA BA DAGA NESA YAKE ZUWA BA✍️✍️✍️

Wani matashi ya tambayi abokinshi, ina kake aiki?

Sai yace: wuri kaza.

Abokin yace : Nawa ake baka a wata?

Yace:- 5000.

Sai abokin yace : 5000 kadai? Tayaya zaka rayu da dubu biyar? 

Tun daga wannan ranar abokin ya raina aikinshi, ya nemi a qara mashi albashi, mai gidan yaqi qara mashi, shi kuma ya watsar da aikin.

A da yana aiki, yana samun 5000 a wata, amma yanzu baya aikin komai.

✍️Wata ta tambayi qawarta wace kyauta mijinki ya baki a ranar birthday dinki?

Sai tace bai bani komai ba.

Shine qawar tace : Da gaske kike? Anya kina da daraja a wurinshi kuwa? 

Tunda ta jefa mata wannan bomb din a gida ta fita, da mijin matar nan ya dawo ya tadda ta cikin fushi, suka hau rigima da jayayya daga qarshe ya sake ta.

Daga ina matsalar ta fara? Daga wannan kalmar da qawarta ta gaya mata.

✍️Ance akwai wani mahaifi da yake rayuwa cikin kwanciyar hankali da iyalanshi, sai abokinshi yace mashi, ya akai danka bai ziyartarka sosai? Anya rashin lokaci ne ko ko dai baya sonka?

Tun daga wannan rana kwanciyar hankalin mahaifin ya qare, ya dawo kallon dukkan abunda danshi yakeyi a matsayin aibi da kuskure, kullum cikin damuwa da rashin godiyar kyautatawar da dandanshi yake mashi.

🌳Tambayoyi ne da zamu iya tsammanin daidai suke, saidai suna iya rusa zamantakewa.

✍️Miyasa baka sayi babbar waya ba?

✍️Miyasa baka mallaki mota ba?

✍️Tayaya zaka riqa jure halayen wannan mutumin?

✍️Tayaya zaka bari ana yi maka wannan abun?

🌳Muna yin wadannan tambayoyin la'alla bisa rashin sani, ko son jin labari, saidai bamu sani ba zasu iya haifar da wasu tambayoyin a zuciyar mai sauraro.

✍️🌹Abunda saqon ya qumsa shine : Karka zamo cikin masu rusa katangar alaqar da take ginanna.

🤝Ka shiga gidan mutane a makance, ka fito a kurmance, babu ruwanka da aibobin cikinsa.

🤝Ba ina wanke kaina bane a lokacin da nake isar da wannan saqon...kuma ba ina nufin ni bana kuskure bane.

Kawai dai nasiha ce nake aikawa zuwa ga kai.

Ina muku fatan alkhairi da kuma barka da War haka...ni matashi ya tambayi abokinshi, ina kake aiki?

Ina muku fatan alkhairi da kuma barka da War haka...

Comments

Popular posts from this blog

TARIHIN SA'ADU ZUNGUR

Ta kaitaccen Tarihin Malam Sa'adu Zungur Dan Siyasa kuma dan Gwagwarmaya, Mawaki. An Haifi Malam Sa'adu Zungur ne a watan Nuwamban Shekarar 1914 a cikin garin Bauchi  Bayan yayi karatun Islamiyya dakuma na Sauran Littatattafan  Addini   Addinin  Musulunci  Malam  Ya halarci  Makarantar Kwaleji  na  yaba dake birnin Legas a  Shekarar 1934 Ya mutu a Shekarar 1958 Marigayi malam Sa'adu Zungur Shine Mutum na Farko daya fara  kafa Jam'iyyar Siyasa a fadin Arewacin Nigeria Malam Sa'adu Zungur Yakasance  Yana daya daga Cikin Shahararrun marubutan  Adabin  harshen hausa  Yakuma kasance dan Siyasa a Lokutan baya. Sa'adu Yasha gwagwarmaya wajen yaki da yadda Turawan mulkin mallaka Suka mulki Kasar Nigeria A Wancan Lokaci. Sannan kuma yakasance mutum  ne mai kaifin basira, Tunani, hazaka dakuma hangen nesa. A Shekarar 1942 ne Yasake dawowa garin bauchi inda yaci gaba da harkar karantarwa. Bayan gamayya dasuka yi d...

Sarkin Biu, Umar Aliyu ya mutu.

Sarkin masarautar Biu a jihar Borno, Mai martaba Mai Umar Mustapha Aliyu ya mutu.  Ya rasu cikin dare a Asibitin lafiya na tarayya (Asibitin Koyarwa na Tarayya), Gombe bayan gajeriyar rashin lafiya.  An haifi HRH Mai Umar a ranar 9th na Nuwamba 1940 a Biu.  Ya halarci makarantar firamare ta Kwaya Kusar Junior tsakanin 1947 zuwa 1949 da Biu Central Primary School daga 1950 zuwa 1953. Daga nan ya tafi makarantar firamare ta Hausari a Maiduguri tsakanin 1953 da 1955.  Ya kasance a lokuta daban-daban ya kasance mai kula da lafiyar dabbobi (1958), Memba mai wakiltar masarautar Biu a Majalisar Masana'antu da Al'adu ta Jihar Borno kuma Hakimin garin Biu daga 1975 zuwa 1989 lokacin da ya zama Sarkin Biu.  Jaridar Neptune Prime ta tattara daga babban dan marigayi, Maina Mustapha Mai Umar, Hakimin na yanzu da kuma Maidala na Biu, cewa marigayi Sarkin ya bar mata hudu da yara sama da saba'in tare da jikoki kusan 200. Allah ya jikan shi da Rahama Ameen.