Skip to main content

TARIHIN SA'ADU ZUNGUR

Ta kaitaccen Tarihin Malam Sa'adu Zungur Dan Siyasa kuma dan Gwagwarmaya, Mawaki.

An Haifi Malam Sa'adu Zungur ne a watan Nuwamban Shekarar 1914 a cikin garin Bauchi  Bayan yayi karatun Islamiyya dakuma na Sauran Littatattafan  Addini   Addinin  Musulunci  Malam  Ya halarci  Makarantar Kwaleji  na  yaba dake birnin Legas a  Shekarar 1934 Ya mutu a Shekarar 1958 Marigayi malam Sa'adu Zungur Shine Mutum na Farko daya fara  kafa Jam'iyyar Siyasa a fadin Arewacin Nigeria

Malam Sa'adu Zungur Yakasance  Yana daya daga Cikin Shahararrun marubutan  Adabin  harshen hausa  Yakuma kasance dan Siyasa a Lokutan baya.

Sa'adu Yasha gwagwarmaya wajen yaki da yadda Turawan mulkin mallaka Suka mulki Kasar Nigeria A Wancan Lokaci.

Sannan kuma yakasance mutum  ne mai kaifin basira, Tunani, hazaka dakuma hangen nesa.

A Shekarar 1942 ne Yasake dawowa garin bauchi inda yaci gaba da harkar karantarwa.

Bayan gamayya dasuka yi dasu Malam Aminu kano  da muhammed baba halla nayin gwagwarmaya  da yadda ake mulki a yankin arewa a wancan zamanin,  Malam sa'adu Zungur yakasance Sakataren Jam'iyyar NCNC a Shekarar 1948.

Malam Sa'adu Zungur yayi Rubuce Rubuce dadama a fannin Adabin hausa.

Wasu daga cikin littattafan daya Rubuta  Wadanda sukafi Shahara Sunhada da.

1. Arewa jamhuriya ko mulukiya.
2. Maraba da Soja.

Yakuma Kasance Abun koyi dakuma kwaikwayo ga sauran marubuta  adabin harshen hausa irinsu, Malam Abubakar ladan Zariya da sauran marubuta adabin hausa.

Yarasu a cikin garin Bauchi a Shekarar 1958 Allah Yajikansa da rahama Amin.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Sarkin Biu, Umar Aliyu ya mutu.

Sarkin masarautar Biu a jihar Borno, Mai martaba Mai Umar Mustapha Aliyu ya mutu.  Ya rasu cikin dare a Asibitin lafiya na tarayya (Asibitin Koyarwa na Tarayya), Gombe bayan gajeriyar rashin lafiya.  An haifi HRH Mai Umar a ranar 9th na Nuwamba 1940 a Biu.  Ya halarci makarantar firamare ta Kwaya Kusar Junior tsakanin 1947 zuwa 1949 da Biu Central Primary School daga 1950 zuwa 1953. Daga nan ya tafi makarantar firamare ta Hausari a Maiduguri tsakanin 1953 da 1955.  Ya kasance a lokuta daban-daban ya kasance mai kula da lafiyar dabbobi (1958), Memba mai wakiltar masarautar Biu a Majalisar Masana'antu da Al'adu ta Jihar Borno kuma Hakimin garin Biu daga 1975 zuwa 1989 lokacin da ya zama Sarkin Biu.  Jaridar Neptune Prime ta tattara daga babban dan marigayi, Maina Mustapha Mai Umar, Hakimin na yanzu da kuma Maidala na Biu, cewa marigayi Sarkin ya bar mata hudu da yara sama da saba'in tare da jikoki kusan 200. Allah ya jikan shi da Rahama Ameen.